AUREN SADIYA HARUNA DA G-FRESH


Soshiyal midiya ta wayi gari yau Jumma'a da labarin auren wasu ýan midiya, waɗanda suka shahara da abubuwa na baɗala da sunan nishaɗantarwa. Bisa ga hotunan da suka bayyana kuma su ma'auratan suka tabbatar a shafukan su, Sadiya Haruna da aka fi sani da Sayyida, da Abubakar Al-Ameen, wanda aka fi sani da G-Fresh sun yi aure.
Wannan ya ƙara nuna cewa, yana iya yiwuwa ýan soshiyal midiya su yi aure. Sai dai fatan Allah Ya sa ma'auratan su ba mara ɗa kunya. Su suturta rayuwar auren su, kuma su nemi gafarar Ubangiji ga laifukan da aka yi ta tafkawa a baya. Don Allah mai rahama ne mai jin ƙai.

©Abba Abubakar Yakubu
             16/06/2023

Comments