Bikin Babban Sallah: Sanata 'Yar'adua ya Rabawa mutanan shiyarsa Naira N24m ga Yan Katsina ta tsakiya



 Sanata Abdul’Aziz Musa Yar’adua mai wakiltar mazabar Katsina ta tsakiya ya bada kimanin Naira Miliyan 24 domin rabawa al’ummar kananan hukumomi 11 na shiyyar da yake wakilta.

 Wadanda  da suka ci gajiyar wannan karimcin sun hada da Shugabannin Jam’iyya a matakin kananan hukumomi da na Unguwa, Manyan Masu ruwa da tsaki, Malamai, da sauran magoya bayansa a fadin yankin Sanata.

 Karimcin da aka riga aka raba shi ne don sanya waɗanda suka ci gajiyar bikin Eid-el-Adha cikin sauƙi.

 Wani makusancin Sanatan Abu Bala Saulawa ya bayyana cewa Sanata ‘Yar’aduwa yana yin hakan tun kafin a zabe shi a matsayin Sanata kuma zai ci gaba da baje kolin irin wadannan ayyuka.

 Wani makusancinsa Tanimu Gwarjo ya bayyana Sanata ‘Yar’aduwa a matsayin mutum wanda ya sadaukar da lokacinsa da dukiyarsa da kuma kwarewarsa wajen kawo ma jama’arsa taimako.

 Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Alhaji Yahaya Asasanta ya bayyana jin dadinsa da wannan gagarumin  aikin.

Comments